Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri ya bayyana cewa, al’ummar Lebanon sun tsallake wani zango wanda shi ne mafi hatsari a tarihin kasar.
Nabih Barri ya kuma kira yi dukkanin mutanen kudancin Lebanon da su koma gidansu a kudancin kasar bayan da ‘yan gwgawarmaya su ka mayar da su wuta mai kona ‘yan mamaya, ko da kuwa za su rayu ne akan baraguzan da aka rusa.
Shugaba majalisar dokokin ta kasar Lebanon ya kuma yi godiya ta musamman ga Shahid al’umma Sayyid Hassan Nasrallah, wanda ya dora mani amanar gwgawarmayar siyasa.
Har ila yau Nabih Barri ya kira yi dukkanin al’ummar kasar sa su cigaba da hadin kai, ya kuma kira yi ‘yan siyasar kasar da su shirya zabar shugaban kasa.
Shi kuwa Fira ministan kasar Najib Mikati ya ce hadin kan da al’ummar kasar su ka nuna a lokacin yaki, ya dakile kokarin tayar da fitinar cikin gida.