Mutum 50 Sun Yi Shahada A Wani Harin Da Isra’ila A Zirin Gaza

Hare-haren bama-bamai da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai a zirin Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane akalla 50 a ranar Talata, kamar yadda hukumar bayar

Hare-haren bama-bamai da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai a zirin Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane akalla 50 a ranar Talata, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta Falasdinu ta sanar, yayin da sojojin Isra’ila ke ci gaba da kai farmaki a Jabaliya.

A cewar ma’aikatar lafiya ta Falasdinu, akalla mutane 17 ne suka rasu a wani harin da Isra’ila ta kai a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Faluja da ke arewacin zirin Gaza.

Wasu 10 kuma sun rasa rayukansu sakamakon hari kan wani gida da makami mai linzami na Isra’ila a Bani Souhaïla, kusa da Khan Younes a kudancin yankin.

Har ila yau wani harin da Isra’ila ta kai ya lalata gidaje uku a birnin Gaza da ke unguwar Sabra.

Masu aikin ceto sun ce sun zakulo gawarwaki biyu daga cikin baraguzan ginin kuma ana ci gaba da neman mutane 12 da ake kyautata zaton suna wurin a lokacin da aka kai harin.

An kashe wasu mutane takwas a sansanin ‘yan gudun hijira na Nusseirat da ke tsakiyar yankin, a cewar ma’aikatan kiwon lafiyar Falasdinu.

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce an kashe wani likita a lokacin da yake kokarin taimakawa mutanen da suka jikkata a harin na al-Faluja.

Dakarun na Isra’ila dai sun kewaye Jabaliya, tare da tura tankokin yaki zuwa garuruwan Beit Lahiya da Beit Hanoun da ke makwabtaka da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments