Jaridar “Ra’ayul-Yau” ta dauki wani labari dake cewa; A yau Litinin kungiyar da take fada da kulla alaka da HKI ta kasar Moroko, ta fitar da wani bayani da a ciki ta yi All,, wadai da yadda aka kyale jirgin ruwan HKI ya yada zango a tashar jiragen ruwa ta garin Tanja, tare da bayyana hakan a matsayin keta hukuncin kotun kasa da kasa ta manyan laifuka.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa tuni ta aike da sakwanni zuwa ga cibiyoyin gwamnatin kasar da lamarin ya shafa saboda a gudanar da bincike akan dalilin da ya sa aka bari jirgin ruwan ‘yan sahayoniyar ya yada zango a daya daga cikin tasoshin jiragen ruwan kasar.
Shugaban wannan kungiyar ta kasar Moroko Ahmad Waihaman ya ce sun yi taron gaggawa na musamman inda su ka yi nazarin hakikanin abinda ya faru, kuma duk wanda yake da hannu dole ya dauki alhaki, domin tarihi ba shi da tausayin bayyana masu laifi.
Al’ummar kasar Moroko suna cikin wadanda suke yin Zanga-zanga da gangami daga lokaci zuwa lokaci domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da yin tir da kisan kiyashin da HKI take yi musu.