Mutanen Kasar Lebanon Suna Tsoron HKI Zata Shiga Kasar Daga Kasar Siriya

Jami’an tsaro a kasar Lebanon sun bayyana damuwarsu da yiyuwar sojojin HKI su farwa kasar da yaki da nufin kwace kasar da kuma sunan yaki

Jami’an tsaro a kasar Lebanon sun bayyana damuwarsu da yiyuwar sojojin HKI su farwa kasar da yaki da nufin kwace kasar da kuma sunan yaki da kungiyar Hizbullah.

Jaridar da nation ta kasar amurka ta bayyana cewa, HKI ta jibje sojojin masu yawa da kuma tankunan yaki a kusa da Jabal sheikh da suka mamaye, don mai yuwa ta fadawa kasar Lebanon ta kuma mamaye gabaci da areawacin kasar kafi ta fuskan kungiyar Hiszullah wacce tafi bada karfinta a kudancin kasar.

Wasu majiyoyin tsaro guda 2  a kasar ta Lebanon wadanda basa son a bayyana sunayen na fadar cewa sojojin HKI a kan iyakar kasar Lebanon da Siriya sun bayyana cewa a hankali a hankali sojojin HKI suna matsowa kusa da kan iyakar kasar da kasar Siriya.

Tun bayan faduwar gwamnatin Bashhar al-Asad jiragen yakin HKI sun ci gaba da yin luguden wuta a yankunan Bika na gabacin kasar Lebanon, wanda ya nuna irin shirin da suke na sake mamayar kasar ta Lebanon.

Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a kan garin Baalabak da yankin bika da sunan wargaza sansanonin cilla makaman Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments