Mutanen Amurka Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyin Bayan Falasdinawa Bayan Tattaunawar Trump Da Natanyahu Dangane Da Gaza

Mutanen kasar Amurka sun fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da korar Falasdinawa daga Gaza ne, bayan taron da yan jaridu na Trump Da Natanyaho a

Mutanen kasar Amurka sun fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da korar Falasdinawa daga Gaza ne, bayan taron da yan jaridu na Trump Da Natanyaho a birnin washintong a jiya Talata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zangar su na rera taken cewa “gaza ba na sayarwa bane”.

Maganganun Trump a baya-bayan nan, dangane da yankin Gaza dai, ya jawo cece-kuce da dama kan al-amiran a duniya,

A birnin Washington dai mutane sun yi ta kawo batun kare hakkin ‘yan kasa’ da kuma tauya hakkin wata al-umma wacce ta yi shekarun fiye 75 tu na neman hakkinta na komawa kasarta, daga kasashen da suke rayuwa, rayuwa irin ta yan gudun hijira na lokaci mai tsawo.

A lokacin tattaunawar dai shugaba Trump ya janye shawarar maida mutanen gaza daga kasarsu zuwa wata kasa daga cikin kasashen larabawa.

Yace dama su ya bukatar ya kwace iko da Gaza sannan ya dauki matakan kula da shi na wani lokaci, bayan ya cire dukkan boma boman da abubuwan facewa  a yankin sannan ya mikawa HKI yankin.

Har’ila yau shugaban ya kasa samun amincewar majalisar dokokin kasar Amurka dangane da wannan shirin nasa.

Rashida Tlaib da Ilham Umar duk musulmi ne Amurkawa yan majalisar dokokin kasar wadanda suka ki amincewa da ra’ayin na shugabaTrump.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments