Asbitoci a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya wadanda suka hada da Asbitin kasa da kuma na Asokoro duk a ciki suke da wadanda suka ji rauni, ko sun mutu bayan da wata motar daukar gas ta yi hatsari a kan gadar Karu a tsakiyar birnin Abuja a jiya Laraba da misalign karfe 7:14 na yamma.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar muta ne 6 sannan wasu da dama sun ji rauni sanadiyyar hatsarin.
Labarin ya nakalto Mr Mark Nyam mai kula da al-amuran gaggawa na hukumar NEMA ta kasa ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne a lokacinda direban motar daukar gas ya burma cikin wasu ababen hawa a kan gadar Karu wanda ya kai ga feshewar tankar gas da yake dauke da shi. Sannan nan da nan wutan ta watsu zuwa wurare da dama kusa da wurin.
Mark ya kara da cewa a halin yanzu dai jami’an tsaro da na ceto daban daban suna aikin tallafawa wadanda abin yashafa da kuma duk wanda yake bukatar taimako a wurin.