Mutane 1,018 ne aka kashe a ci gaba da kisan kiyashi kan tsiraru a gabar tekun Syria

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar da rahoton cewa, adadin fararen hula da aka yi kisan kiyashin

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar da rahoton cewa, adadin fararen hula da aka yi kisan kiyashin na baya-bayan nan daga tsiraru ‘yan Alawite ya kai mutane 1,018 tun daga ranar alhamis zuwa wannan Lahadi.

Kungiyar sa ido ta ce jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria da kuma kungiyoyin da suke kawance da su da suka da alaka da alkaida, sun kashe fararen hula 745 na Alawi a cikin kwanaki uku da suka gabata, wanda ya haura adadin da aka sanar a lokutan baya.

Sai dai Fox News ta buga misali da wata ‘yar Alawiyya, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa sama da mutane 4,000 ne aka kiyasta an kashe a yankin gabar tekun Syria da kuma cikin ‘yan  Alawiyya.

Kungiyar masu tsatsauran ra’ayin ta Hay’at Tahrir al-Sham wadda ke shugabanci a halin yanzu a Syria, wadda kuma it ace tare da taimakon Turkiya da Amurka da wasu kasashen larabawa ta jagoran jagoranci hare-haren da suka kai ga kawo karshen gwamnatin Assad, ta ce za ta kare tsiraru a kasar, a daidai lokacin da ‘yan bindiga da ke karkashin ikonta a halin yanzu suke yi wa fararen hula yankan rago da sunan cewa suna da alaka da tsohuwar gwamnatin Assad.

Kungiyar sa ido da kare hakkokin dan adam a Syria ta bayar da rahoton ayyukan kisan gilla da dama a cikin ‘yan kwanakin nan, tare da kashe mata da kananan yara.

“Yawancin wadanda aka kashe din an kashe su ne ta hannun wasu da ke da alaka da ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida na sabuwar gwamnatin Syria,” in ji rahoton kungiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments