Rahotanni Daga Gaza sun ce adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da safiyar yau sun haura 200
Wata sanarwar da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta fitar a yau Talata ta ce; Adadin shahidan sanadiyyar sabbin hare-haren HKI sun kai 244.
Sai dai har yanzu ba a kammala tantance adadin adadin shahidan ba, da kuma wadanda su ka jikkata.
Gabanin wannan harin na safiyar yau, an bayyana cewa fiye da Falasdinawa 150 ne su ka yi shahada tun bayan tsagaita wutar yaki.
Babban jami’i mai kula da harkokin watsa labaru a yankin Gaza Isma’ila Sawabita ya sanar da cewa; Tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 19 ga watan Janairu zuwa yanzu adadin Falasdinawa da su ka yi shahada sun haura 150, daga cikinsu har da na bayan nan su 40.
Wannan sanarwar dai ta biyo bayan kisan gillar da ‘yan mamaya su ka yi wa wasu Falasdinawa su 3 a gabashin sansanin ‘yan hijira na “al-Burj’ dake gundumar tsakiya.
Al-sawabita ya kuma tabbatar da cewa; Abinda ‘yan mamaya suke yi, shi ne keta tsagaita dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar tsagaita wutar yaki,ta hanyar ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi.
Haka nan kuma jami’in na watsa labaru a Gaza ya ce; A lokacin da ‘yan mamayar suke ci gaba da yin kisa, suna kuma kirkiro karairayi domin kare abinda suke yi,amma abinda yake faruwa a kasa yana tabbatar da aniyarsu ta tafka laifuka.
Al-Sawabita ya kara da cewa; Dukkanin Falasdinawan da ‘yan mamayar ya kashe ba su yin wata barazana ta tsaro ga sojojinsu.”
A wani gefen, jami’in watsa labarun na Gaza ya yi gargadin cewa da akwai gine-gine masu yawa da suke gab da rushewa saboda farmakin da ‘yan mamaya su ka kai musu a lokacin yaki. Ya kuma kara da cewa; wadannan gine-ginen suna a matsayin barazana ga dubban mazaunan cikinsu a halin yanzu.