Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya isa birnin birnin Jidda na kasar Saudiya tare da tawagarsa don halattan taron gaggawa na kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kafin taron dai ministan ya tattauna da ministocin harkokin wajen kasashen Saudiya da Qatar, dangane da bukatar taron, saboda kissan shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniya wanda HKI ta yi a birnin Tehran bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan.
Taron wanda za’a gudanar da shi a matakin ministocin harkokin waje, zai tattauna dangane da ci gaba da kissan Falasdinawan da HKI take yi a Gaza da sauran wurare da kuma kissan Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar Hamas a Tehran, har’ila da kuma keta hurumin JMI da ta yi da kissan Haniya a Tehran.