Mataimakin shugaban kasar Iran Muhamamd Riza Arif ya bayyana cewa, A halin yanzu ba ya cikin shirin gwamnatin Iran yin ganawa a tsakanin shugaban kasa Mas’ud Fizishkiyan da takwaransa na Amurka Donald Trump.
A jiya Laraba ne mataimakin shugaban kasar Iran Riza Arif da ya yi Magana da ‘yan jarida inda yake mayar da martani akan fatan shugaban kasar Amurka Donald Trump na ganawa da shugaba Mas’ud Fizishkiyan na Iran, yana mai kara da cewa hakan ba ya cikin shirin gwamnati a wannan lokacin.
Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya kuma ce, ya kamata Trump ya san cewa, bisa fatawa ta addini da jagoran juyin musulunci ya fitar, Iran ba za ta mallaki makamin Nukiliya ba.
Riza Arif ce Iran tana cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya ne a cikin fagagen da ba na soja ba.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya rattaba hannu akan dokar sake matsin lamba mai tsanani akan Iran,wacce a zangon shugabancinsa na farko ya yi amfani da shi.
Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya kuma kara da cewa; Mu ba ‘yan ina-da yaki ba ne,amma kuma za mu kare kanmu da karfi mu kuma tanadi mukaman da muke bukatuwa da su.