Mufti ‘Yan Shi’a A Lebanon: Hadin Kai Tsakanin Musulunci Da Kiristanci Shi Ne Tushen Rayuwar Lebanon

Muftin ‘yan Shi’a a kasar Lebanon ya jaddada cewa: Haɗin kai tsakanin  Musulunci da Kiristanci shine tushen rayuwar Lebanon Muftin ‘yan shi’a na kasar Labanon,

Muftin ‘yan Shi’a a kasar Lebanon ya jaddada cewa: Haɗin kai tsakanin  Musulunci da Kiristanci shine tushen rayuwar Lebanon

Muftin ‘yan shi’a na kasar Labanon, Sheikh Ahmed Qabalan, ya jaddada cewa: Kawancen Musulunci da Kiristanci shi ne tushen rayuwar Lebanon, kuma kokarin duk wani bangare na yin galaba a kan dan uwansa lamari ne da zai kai ga kona kasar, kuma batun tantance sunayen shugaban kasa dole ne a yi la’akari da yarjejeniyar da aka amince da ita, kuma kalubalen ya Sanya al’ummar karfafa shingen hana rarraba.

A cikin wata wasika da ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata zuwa ga Yan Majalisar kasar da shugabannin siyasa a Lebanon, Sheikh Qabalan ya yi kira da a kawo karshen matsalar da ta take addabar kasar tare da yin babban illa Lebanon, kuma a lokaci guda ya gode wa jagororin siyasa da suka tashi tsaye da cikakkun manufofinsu na goyon bayan Lebanon da kuma fa’idar kare muradun kasa.

Sheikh Qabalan ya jaddada a cikin sakon nasa cewa: Babbar nasarar da za a samu ita ce hadin kai da amincewar kasar Lebanon kan amintaccen mutum da zai jagorance su, kuma ranar zaman zaben shugaban kasa ta karato sosai, don haka abin da ake bukata shi ne aminci da duba girman kasa da kuma kasancewar al’ummar Lebanon dangi guda da ba zasu yarda da rarrabuwar kawuna da bullar rikici a tsakaninsu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments