A jiya Laraba ne dai sabon shugaban kasar Daniel Chapo ya saba layar rantsuwar fara aiki a matsayin shugaban kasar na biyar a wani gagarumin taro da mutane 2,500 su ka halarta a birnin Maputo.
‘Yan hamayyar siyasar sun yi Zanga-zangar ne a kusa da wurin da ake yin bikin rantsar da sabon shugaban kasar, sai dai hare-haren bindigogi a cikin iska da jami’an tsaro su ka yi, ya hana su isa wurin bikin.
Jami’an tsaron dai sun zagaye wurin da aka yi bikin ranstar da sabon shugaban kasar Chapo dan shekaru 48, wanda a jawabinsa ya yi kira da samar da tsaro da zaman lafiya a cikin wannan kasa ta Kudancin Afirka.
A cikin watan Disamba ne dai majalisar tsarin mulki ta kasar ta bayyana Chapo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar wanda ya lashe kaso 65.17%. Kotun ta yi watsi da karar da jagoran hamayya Venancio Mondlane ya da riya cewa shi ya lashe zaben, ba Chapo wanda ya sami kaso 24% na jumillar kuri’un da aka kada ba.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na cikin gida da kuma waje sun ce, a tsawon lokacin da aka dauka ana yin Zanga-zangar nuna kin amincewa da sakamakon zaben, jami’an tsaro sun kashe a kalla mutane 300 da su ka hada da kananan yara.