Ministocin Harkokin Wajen Iran da Rasha sun Tattauna Gabanin Taron Gwamnonin IAEA

Ministocin harkokin wajen Iran da na Rasha sun tattauna ta  wayar tarho gabanin taron kwamitin gwamnonin IAEA A yayin tattaunawar Araghchi da Lavrov, sun yi

Ministocin harkokin wajen Iran da na Rasha sun tattauna ta  wayar tarho gabanin taron kwamitin gwamnonin IAEA

A yayin tattaunawar Araghchi da Lavrov, sun yi musayar ra’ayi kan batutuwa daban-daban, ciki har da rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan, tare da jaddada muhimmancin yin shawarwari don warware batutuwan da ba su dace ba.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya kuma jaddada bukatar tuntubar juna tsakanin Iran da Rasha da ma sauran kasashen duniya domin lalubo hanyoyin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

A yayin da yake ishara da matakin da Amurka da kawayenta na Turai suka dauka a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dangane da Falasdinu, da wani daftarin kuduri na kafa rundunar kasa da kasa a Gaza, Araghchi ya ce irin wannan shiri ba zai yi nasara ba saboda ya saba wa ka’idojin ‘yanci da hakkin al’ummar Palasdinu na cin gashin kansu.

Lavrov ya bayyana aniyar Moscow na ci gaba da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu da na shiyya-shiyya, da nufin tabbatar da tsaro ta hanyar hadin gwiwa da juna.

Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra’ayi kan hadin gwiwar Iran da hukumar ta IAEA, inda suka jaddada wajabcin ci gaba da tuntubar juna da yin aiki tare tsakanin Tehran, Moscow, da Beijing a wannan fanni.

Wannan ya biyo bayan ganawar da wakilan kasashen Sin da Iran da kuma Rasha suka yi ne da babban daraktan hukumar Rafael Grossi da tawagarsa a taron kwamitin gwamnonin na IAEA mai zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments