Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana cewa za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ayyukan hadin gwiwa ta fuskar tsaro tsakanin Iran da Syria.
Nasirzadeh ya bayyana haka ne ga manema labarai yayin da ya isa babban birnin kasar ta Siriya a yammacin jiya Asabar tare da wata babbar tawaga ta manyan jami’ai a bangaren ayyukan tsaro.
“Za mu gana da manyan jami’an siyasa da na soji don yin nazari kan bangarori daban-daban na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tare da mai da hankali musamman kan harkokin tsaro da na soja,” in ji ministan tsaron na Iran.
“Manufarmu ita ce gano dabarun inganta wadannan bangarorin. Da fatan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta bunkasa ta yadda za mu iya taimakon juna a cikin yanayin da ake ciki.”
Ya kuma bayyana cewa, Syria na da matsayi mai muhimmanci a harkokin wajen Iran, yana mai cewa ya ziyarci Damascus ne bisa gayyatar takwaransa na Syria.
A ziyarar tasa ta kwanaki biyu, babban hafsan tsaron na Iran zai gana da shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, da ministan tsaron kasar Laftanar Janar Ali Mahmoud Abbas da sauran jami’an soji da na siyasa.
Bangarorin biyu za su tattauna kan rawar da kasashen yankin za su iya takawa wajen tabbatar da tsaro a yankin, da janyewar sojoji kasashen ketare masu yin kutse a cikin lamurran tsaro na kasashen yankin.