Ministan Tsaro Na Kasar Iran ya bada Labarin Gwajin Wani Sabon Makami Mai Limzami Mai Daukar abubuwan Fashewa Har Ton Biyu

Ministan tsaro na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin kasar sun yi gwajin wani makami mai linzami wanda yake iya daukar abubuwan fashewa hart un

Ministan tsaro na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin kasar sun yi gwajin wani makami mai linzami wanda yake iya daukar abubuwan fashewa hart un biyu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Amir Nasirzade yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa . wannan gwajin sako ne ga gwamnatin Amurka da kawayenta. Idan wani ya dora mana yaki sai sun fi mu shan wahali. Don tare da wadannan shirye shiryen da kuke na kare kammu sai mun kori amurka daga yankin nan.

Yace iran tana cikin fushi kan abinda yake faruwa a Gaza don haka duk wata dama da ta samu zata maida martanin da ya dace. Ministan ya bayyana haka ne a jiya Laraba bayan taron Majalisar ministoci tare da shugaban kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments