Siyasar tsananata matsin lamba kan Iran ta gaza cimma buri kuma hana fitar da man da Iran ke fitarwa mafarki ne da ba zai tabbata ba
Ministan mai na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana matsayar matsin lamba da Amurka ke yi kan fitar da man kasar Iran a matsayin siyasa ta nuna gazawa, yana mai cewa: Hana fitar da man fetur din Jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa wajen kasar, mafarki ne da ba zai taba wanzuwa ba.
Ministan mai na Iran Mohsen Paknejad a matsayin mayar da martani ga furucin Trump ta sake dawo da tsananta siyasar matsin lamba da nufin gurgunta harkar tattalin arzikin Iran ta hanyar hana ta fitar da man fetur, a jiya Lahadi ya bayyana furucin a matsayin mafarki da ba zata tabbata ba, kuma baya da hakkin hana Iran gudanar da harkokinta na harkar mai har abada saboda mafarki ne maras yiwuwa.
Mohsen Paknejad ya jaddada cewa: Wannan manufar siyasa ce da zata gaza cimma nasara. Ministan yana mai jaddada cewa: A irin yanayin da kasar Iran take ciki, masana’antar mai da kwararrun da ke aiki a bangaren fitar da man fetur, babu shakka za su dauki matakai na musamman da suka dace, inda ya kara da cewa: Duk lokacin da aka kara takura wa Iran, matakan da take dauka su kan kara sarkakiya kan makiya.