Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya iso birnin Tehran a jiya lahadi kuma ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar iran Abbas Araqchi.
Ziyarar tasa ana saran za ta kara fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ganin cewa dukkan kasashen biyu suna taka rawa a batutun da suka shafi yanki dama duniya baki daya.
Bugu da kari bayan ganawarsa da Araqchi da musayar ra’ayoyi kan batutuwa daban daban, zai gana da sauran manyan jami’an gwammnatin kasar, da ake saran za su tattauna kan alakar dake tsakaninsu da kuma irin ci gaban da aka samu a yankin da dai sauran batutuwa na kasa da kasa.
Ana sa bangaren shugaban kasar iran Masud pezeshkiyan a lokacin ganawarsa da Hakan fidan ministan harkokin wajen kasar turkiya ya jaddada game da muhimmancin hadin kan kasashen musulmi cikin gaggawa, yace ya kamata kasashen musulmi su rike duba yanayi da yan uwansu suke ciki, kuma a nisanci tsaurara alamura, adaidai lokacin da suke fuskantar matsin lamba daga kasashen waje.