Ministan Harkokin Wajen Rasha Ya Mika Alhininsa Na Rasuwar Sayyid Ra’isi A Ofishin Jakadancin Iran

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi ta’aziyya kan rayuwar shugaban kasar Iran a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Moscow Ministan harkokin wajen

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi ta’aziyya kan rayuwar shugaban kasar Iran a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Moscow

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya halarci ofishin jakadancin Iran da ke birnin Moscow a jiya Laraba, inda ya rattaba hannu kan takardar ta’aziyya ga shahidan da suka yi hatsari a jirgin saman shugaban kasar, ya kuma yi jinjina ga shugaban kasar Iran Hujjatul-Islam Ibrahim Ra’isi, da ministan harkokin wajen kasar ta Iran Hossein Amir Abdollahian.

Tun da farko dai, wakilan majalisar dokokin Rasha (majalisar Duma da na Tarayyar), tare da rakiyar wasu manyan jami’an Rasha da suka hada da ma’aikatun harkokin cikin gida da tsaron kasar, sun sanya hannu kan takardar ta’aziyyar rasuwar jami’an na Iran tare da tunawa da su. Jirgi mai saukan ungulu na shugaban kasar Iran dai ya yi hatsari ne a shiyar  arewa maso yammacin kasar Iran, inda dukkan mazauna cikinsa suka yi shahadaa ranar Lahadin da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments