Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce, yayi mamakin yadda sojojin kasar Siriya suka ki yakar yan bindiga har suka kwarce iko da kasar ba tare da wata turjiya ko kadan ba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a jiya a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, a karshen haduwarsa da shugaban Bashar Asad yayi korafi dangane da sojojin sa.
Ministan ya kara da cewa aikin sojojin kasar Siriya su kare kasarsu daga mamaye, don al-amari ne na cikin gida. Don haka Iran bata ganin ya zama wajibi a kanta ta kare kasar Siriya daga mamayar wani. Sannan gwamnatin kasar bata bukaci kasar Iran ta yi hakan ba.
Ministan ya kammala da cewa kafin faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad mun fadawa gwamnatin dangane da yiyuwan wadan nan yan ta’adda su yi kokarin mamayar kasar, don haka bamu abinda yasa basu dauka matakan da suka dace na kare kasar daga faduwa hannun yana ta’ada ba.
A taron kasashen samar da zaman lafiya a kasar Siriya Iran, Turkiyya da kuma Rasha sun amince a taron daoha kan cewa za’a warware matsalar ta hanyar siyasa.