Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauna Da Tokwaransa Na Kasar Turkiya Dangane Da Sake Bullar Yan Ta’adda A Kasar Siriya

Minitosin harkokin wajen kasashenr Iran da turkiyya, Abbas Aragchi da Hakan Fidan sun tattauna a tsakninsu danganew da sake bullar yan ta’adda a kasar Siriya

Minitosin harkokin wajen kasashenr Iran da turkiyya, Abbas Aragchi da Hakan Fidan sun tattauna a tsakninsu danganew da sake bullar yan ta’adda a kasar Siriya a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Abbas Aragchi ya isa birnin Ankara babban birnin kasar Turkiyya ne a safiyar yau Litinin bayan ya yada dan gajeren zazngo a kasar Siriya.

Bangarorin biyu sun tattauna kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma matsalolin yankin daga ciki har da sake bullar yan ta,adda a arewacin kasar Siriya.

A lokacinda yake hira da yan jaridu a lokacin isarsa Ankara, Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran takan shawarci kasar Turkiya dangane da duk abinda ya shafi yankin, musamman dangane da yan ta’adda wadanda suke mamaye da wani bangare na kasar Siriya tun shekara ta 2014.

Ministan ya kara da cewa Iran bata son kasar Siriya ta sake zama matattarn yan ta’adda a yankin. Kuma zaman lafiya tsakanin kasashen biyu da kuma yankin yana da matukar muhimmanci.

Kafafen yada labarai na kasar Siriya sun bayyana cewa sojojin kasar sun kashe Karin yan ta’adda 320 a yakin da suke fafatawa  da yan ta’adda a yankunan Halab, idlib da kuma Hama.

Ya zuwa yanzu dai jimillar yan ta’adda kimani 1,300 suka halaka a hare-haren da sojojin Siriya da na Rasha suka kai masu a yankunan da suke iko da su a cikin kimani mako guda da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments