Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa brnin Beijing na kasar China a safiyar yau Jumma’a. Ya kuma bayyana cewa manufar zuwarsa kasar China ita ce tattaunawa mai muhimanci tsakanin kasashen biyu, wadanda kuma sunka shafi shirin nukliyar kasar ta Iran da kuma batun sauye sauyen da ke faruwa a duniya musamman a gabas ta tsakiya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Aragchi ya je kasar China ne tare da gayyatar tokwaransa na kasar, kuma tattaunawarsu zai hada da batun shirin nukliyar kasar Iran da kuma shirin da kasashen turai da Amurka suke da shin a sake farfado da takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa Iran a cikin kuduri mai lamaba 2231. Har’ila yau da kuma muhimman al-amuran da ake zaton zasu faru a cikin shekara mai klamawa ta 2025.