Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tsananta matsin lamba da ake son dauka kan Iran ba zai yi wani tasiri ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Manufar matsin lamba da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka kan Iran za ta sake yin kasa a gwiwa tare da rashin nasara.
Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan kammala zaman majalisar ministocin a yau Laraba, inda ya ce mafi girman matsin lamba shi ne gwajin da aka yi kan kasar Iran da bai yi nasara ba, ya kara da cewa; Idan babban batu shi ne cewa Iran ba ta kama hanyar mallakar makamin nukiliya ba, to hakan na iya yiwuwa kuma babu wata matsala a wannan bangaren.
Araqchi ya jaddada cewa: Matsayin Iran a bayyane yake, kuma ita mamba ce ta NPT (yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya) kuma fatawar Jagoran juyin juya halin Musulunci tana da inganci da kuma bayyana irin nauyin da ke wuyan kasar ta Iran.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a yammacin jiya Talata bayan sanya hannu kan wata doka mai dawo da manufar matsin lambar siyasa kan kasar Iran cewa: Za su kakaba wa Iran “takunkumi mai tsanani” tare da dakatar da fitar da man da take fitarwa.