Ministan Harkokin Wajen Iran Zai Tattauna Ta Wayar Tarho Da Takwarorinsa Na Kasashen Turai

Ministan harkokin wajen kasar Iran zai gudanar da tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na kasashen Turai uku Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail

Ministan harkokin wajen kasar Iran zai gudanar da tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na kasashen Turai uku

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi zai gana da ministocin harkokin wajen kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da kuma wakilin kungiyar tarayyar Turai a yau Juma’a ta hanyar wayar tarho. Game da sabon ci gaban da aka samu a shawarwarin da aka cimma tsakanin Iran da Turai kan batun makamashin nukiliyar Iran.

Ismail Baqa’i ya ce: Bisa hadin kai da aka yi, ministan harkokin wajen kasar Iran zai yi wata ganawa ta hanyar wayar tarho tare da ministocin harkokin wajen kasashen Faransa, Birtaniya, da Jamus, da kuma babban wakilin kungiyar Turai Kaya Kalas, a yau Juma’a.

Baqa’i ya kara da cewa: A yayin wannan kiran ta hanyar wayar tarho, za a tattauna batun Shirin makamashin nukiliyar Iran da kuma bukatun kasar Iran, musamman dangane da batun dage takunkumin rashin adalci da kuma wajibcin hukunta bangarorin da ke da hannu wajen kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted