Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ci gaba da ake samu a shawarwari makamashin nukiliyar Iran tsakanin Amurka da Iran amma ana buƙatar gaskiya da hangen nesa daga ɗayan ɓangaren
A yammacin jiya Juma’a ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, inda suka yi musayar ra’ayi da musayar mahanga da kuma tattaunawa kan ci gaban yankin da kuma kasa da kasa. Araqchi ya kuma yi wa Guterres bayani kan sabbin abubuwan da ke faruwa a shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, da kuma shirye-shiryen da masarautar Oman ta yi na tsara zagaye na gaba na wadannan shawarwari.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi nuni da matakin daukar nauyi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi wajen zabar tafarkin diflomasiyya don warware takaddamar shirinta na makamashin nukiliya ta hanyar lumana, yana mai jaddada cewa, ci gaba kan wannan tafarki na bukatar kuduri na gaskiya da hangen nesa daga daya bangaren. Ya jaddada cewa Iran a matsayinta na mamba a yerjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi, ta himmatu wajen aiwatar da alkawurran da ta dauka, sannan ta dage kan hakkin al’ummar Iran na amfana da makamashin nukiliya domin zaman lafiya, wanda ke bukatar hakkin sarrafa sinadarin yuraniyom.