Ministan harkokin wajen Iran ya bayyanam cewa: Iran tana ci gaba da mutunta yarjejeniyar hana samar da makaman kare dangi kuma lamarin a fili yake ga kowa da kowa
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Araqchi ya rubuta a shafin sadarwa na dandalin X cewa: “Tsarin da Iran ta dade tana tafiya a kai na yarjejeniyar hana yaduwar makamai ta duniya (NPT) a fili yake ga kowa da kowa, kuma Iran ta sanya hannu kan yarjejeniyar ta NPT tun a shekara ta 1968 a matsayin daya daga cikin kasashen duniya da suke membobi a samar da yarjejeniyar da mutunta ta a duniya.
Sanarwar ta Araqchi ta zo ne a matsayin martani ga furucin baya-bayan nan da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi ne, inda ya ce, “Dole ne Iran ta bayyana karara cewa tana ci gaba da yin watsi da batun mallakar makamin nukiliya.”
Araqchi ya rubuta a shafinsa na sadarwa na dandalin X, cewa: “Ba abin kunya ba ne a gare su shawartar Iraniyawa, kuma ya kamata Iran ta ci gaba da jaddada matsayinta a fili cewa har abada ba ta bukatar mallakar makamin nukiliya a fagen tsaron kai.