Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da takwaransa na Qatar a gefen taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Doha.
Doha ta sanar da cewa, fira ministan kasar Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar ya yi nazari kan al’amuran yankin na baya-bayan nan yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi.
A yayin wannan taro, harin da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a birnin Doha shi ne babban abin da ake tattaunawa akai.
Araqchi yayi Allah wadai da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai, yana mai tabbatar da goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma goyon bayan gwamnati ga al’ummar Qatar.
A cikin wannan yanayi, Araqchi ya gana tare da tuntubar ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan da ministan harkokin wajen Pakistan Muhammad Ishaq Dar a gefen taron kasa da kasa a birnin Doha.
An gudanar da wadannan tarukan ne domin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da kuma tattauna batutuwan da suka shafi yankin.