Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa zai tafi birnin Roma a ranar Asabar domin halartar zagaye na biyu na shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai jaddada cewa sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha ya kunshi muhimman batutuwa.
A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA, Araghchi ya ce: Roma ba ita ce mai masaukin baki ba, a’a, a maimakon haka, wajen da za a yi shawarwarin, gwamnatin Oman ce ta kasance mai daukar nauyin shawarwarin ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, kuma Iran za ta kasance a wurin da mai masaukin bakin ya kayyade, aikin shiga tsakani da kulla huldar da ba na kai tsaye ba, shi ne alhakin gwamnatin masarautar Oman.”
Ya kara da cewa, “Zai tafi Roma ranar Asabar kuma za a fara zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka.
Arakchi ya ce: Rasha da sauran kasashe sun bayyana aniyarsu ta taimaka wajen ciyar da shawarwarin gaba.