Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI zata ci gaba da kasancewa tare da al-ummar Falasdinu a fafatawar da suke yi da sojojin HKI tun watanni 11 da suka gabata, ya kuma kara da cewa nasara ta karshe zata kasance tare da falasdinawan ne.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a cikin zantawarsa ta wayar tarho da matainakin shugaban kungiyar Hamas a bangaren harkokin siyasa Khalid Alhayya a yau Laraba. Banda haka ministan ya kara da cewa, gwamnatin kasar Irann a wani bangare tana kokarin ganin an tsagaita budewa juna wuta a Gaza, tsagaita wuta wanda zai amfani mutanen Gaza