Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasarsa A Shirye Take Ta Sulhunta Tsakanin Pakistan Da Indiya

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta inganta fahimtar juna tsakanin Indiya da Pakistan Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta inganta fahimtar juna tsakanin Indiya da Pakistan

Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya sanar a yau Juma’a cewa: kasarsa a shirye take ta yi aiki mai kyau a fagen sulhunta tsakanin Indiya da Pakistan don inganta fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu a wannan mawuyacin lokaci.

Da yake tsokaci game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan tsakanin Indiya da Pakistan, Araqchi ya bayyana cewa: “Indiya da Pakistan kasashe ne ‘yan uwan ​​juna kuma masu makwabta da Iran, kuma suna da alakar al’adu da wayewa tun shekaru aru-aru.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa: “Suna daukar kasashen Indiya da Pakistan a matsayin sauran makwabtansu, kuma masu matsayin fifiko na farko.” Don haka Iran a shirye take ta yi amfani da dukkanin kwarewarta wajen kyautata alaka tsakanin Pakistan da Indiya, don inganta fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu a cikin wannan lokaci mai wuyar gaske.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments