Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kasar Siriya na cikin mawuyacin hali na gwaji
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Shakka babu duniyar musulmi ta damu matuka kan makomar yankin yammacin Asiya, bisa la’akari da yanayin da ake ciki a kasashen Siriya da Falastinu.
Araqchi ya rubuta a cikin wata makala da aka buga a jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon cewa: Siriya a yau tana cikin gwaji mai wahala. Sannan akwai barazanar da ke tattare da yunkurin kungiyoyin ta’addanci irinsu Al-Qaeda da ISIS, kuma hakan ya kara dagula al’amura a yankin.
Al’ummar wannan yanki suna da muhimmiyar rawar da zasu taka wajen tsara makomar siyasar duniyar Musulunci, domin kuwa a cikin shekaru aru-aru an fuskancin ire-iren wadannan matsaloli kuma an samu nasarar magance su, kamar yadda a wasu shekaru masu yawa aka fuskanci munanan hare-hare da ya biyo bayan rikicin Yahudawa da Kiristanci na Turai, wanda ya bazu zuwa yankin nan bayan yakin duniya na biyu, musamman saboda rashin mutunta hakkin al’ummar wannan yanki.