Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Iran Zata Kalubalanci Duk Wanda Ya Kai Hari Kan Cibiyoyin Nukiliyarta

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Duk wani hari da aka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai fuskanci mayar da martani cikin gaggawa Ministan

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Duk wani hari da aka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai fuskanci mayar da martani cikin gaggawa

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Harin da Amurka da yahudawan sahayoniyya suke kai wa kan cibiyoyin nukiliyan kasashe, nau’in hauka ne kuma zai jefa yankin cikin bala’i.

A cikin wata sanarwa da ya aikewa gidan talabijin na Sky News a ranar Talata, Araqchi ya sake jaddada matsayin Iran na cewa: “Duk wani hari da za a kai wa cibiyoyin nukiliyar kasarsa zai fuskanci mayar da martani cikin gaggawa da azama,” ya kara da cewa: “Ba ya jin za a aiwatar da irin wannan aikin wauta kan Iran, hasali ma, hakan wani nau’in hauka ne kuma zai wurga yankin cikin mummunan bala’i.”

Dangane da yiwuwar tattaunawa da Amurka da kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da warware takaddamar ta hanyar diflomasiyya, Araqchi ya jaddada cewa: “Sabuwar yarjejeniyar da za a kulla da Iran zata kasance mai kyau.” Ya kara da cewa: yanayi ya canja da matakan baya saboda akwai ayyuka masu yawa wanda dole ne ga ɗaya bangaren ya ɗauki matakin dawo da kwarin gwiwa, duk da har yanzu Iran ba ta ji komai daga gare shi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments