Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ta cika hakkinta, yanzu kuma turai ne ake jiran ta cika nata hakkokin
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa, a wani mataki da Iran ta dauka na nauyin shiga tattaunawa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, domin tsara wani sabon daftarin aiki mai ma’ana kan yadda za a aiwatar da alkawuran da ta dauka na kare hakkokin da suka hau kanta, yanzu kuma ana jiran Turai ta cika nata alkawuran.
A wata tattaunawa ta wayar tarho tare da ministocin harkokin wajen Faransa, Jamus, da Birtaniya, da kuma jami’in kula da harkokin waje na EU, Araqchi ya ce: “Dole ne sauran bangarorin su yi amfani da wannan damar wajen ci gaba da gudanar da harkokin diflomasiyya don kaucewa rikicin da za a iya afkawa, da kuma nuna muhimmancinsu wajen neman hanyar diflomasiyya da kuma imanin da suke da shi na samar da mafita ta hanyar zaman lafiya.”
Araqchi ya yi nuni da cewa yunkurin da kungiyar kasashen Turai Troika ke yi na mayar da takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran ba shi da wata ka’ida ta doka ko ta dabi’a, yana mai jaddada cewa kiyaye yanayin tattaunawa da diflomasiyya yana da matukar muhimmanci don kaucewa tabarbarewar lamarin.