Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Dangantakar Iran da Lebanon tarihi ce, mai tushe, kuma ta ginu ne bisa mutunta juna
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana alakar da ke tsakaninta da kasar Lebanon a matsayin mai tarihi, mai tushe, kuma ta ginu ce bisa mutunta juna. Ya ce: “Kasashen biyu sun kuduri aniyar bunkasa wannan alakar.
A jawabin da ya yi a filin jirgin sama na birnin Beirut, inda wakilin kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon ya tarbe shi, Araqchi ya yi nuni da cewa ziyarar wani bangare ne na rangadin da yake yi a yankin bayan ziyarar da ya kai birnin Alkahira na Masar, kuma zai gana da jami’an kasar ta Lebanon.
Ya kara da cewa, alakar Iran da Lebanon ta kasance mai tarihi, mai tushe, kuma ta ginu ce bisa mutunta juna, sannan Iran ta kuduri aniyar raya wannan alakar. Ya kara da cewa, Suna ba wa ‘yantacciyar kasar Lebanon matukar muhimmanci da kuma ba da goyon bayansu wajen tunkarar ‘yan mamaya.
Ministan harkokin wajen na Iran ya ci gaba da cewa: A ko da yaushe suna goyon bayan ‘yancin kan kasar Lebanon a kowane mataki, kuma suna ci gaba da ba ta goyon baya a cikin mawuyacin halin da ake ciki.