Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce Abin Da Ke Faruwa A Siriya Aikin Amurka Da Isra’ila Ne

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Abin da ya faru a Siriya ya zo ne a matsayin wani babban aiki da Amurka da

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Abin da ya faru a Siriya ya zo ne a matsayin wani babban aiki da Amurka da Isra’ila suka tsara

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Abin da ya faru a kasar Siriya ya zo ne a cikin tsarin wani gagarumin aiki da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suka shirya domin kawar da duk wata gwagwarmaya da take adawa da mamayar yahudawan sahayoniyya.

A wata hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-Ghad ta kasar Masar, ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gabatar da wani kuduri kan kungiyoyin gwagwarmaya ba, kuma ba ta yi kokarin neman tsoma baki a cikin harkokin kasar Siriya ba, kuma shawarar kasancewar a cikin kasar ya zo ne bisa gayyatar gwamnatin Bashar al-Assad domin yakar kungiyoyin da suke dauke da makamai.

Araqchi ya kara da cewa: Iran ta shiga kasar Siriya ne bisa bukatar gwamnatin kasar don tunkarar kungiyoyin ‘yan ta’adda, kuma ba ta tsoma baki a cikin harkokin da gwamnatin Siriyan take yi wajen gudanar mu’amalarta al’ummarta ko kuma ‘yan adawa.

Araqchi ya yi nuni da cewa: Iran ta shiga kasashen Siriya da Iraki ne bisa gayyatar da gwamnatocin kasashen biyu suka yi mata domin yakar ta’addanci, musamman yaki da kungiyar ISIS, inda ya kara da cewa “Lokacin da aka kawar da wadannan kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasashen biyu, Iran ta fice daga cikin kasashen kuma ba ta da wani nau’i na tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments