Ministan harkokin wajen Holland Casper Veldkamp ya sanar da murabus dinsa a ranar Juma’a, yana mai nuna rashin amincewa da abin da ya bayyana a matsayin dakile yunkurinsa na kara daukar matakai da matsin lamba kan Isra’ila.
Veldkamp ya fada a cikin wata sanarwa a hukumance cewa gwamnatin Holland ta riga ta dauki matakai masu muhimmanci, ya kara da cewa, “Na lura da cewa a cikin gwamnati akwai masu adawa da daukar karin matakai kan Isr’ila sakamakon abin da ke faruwa a Gaza da kuma yammacin gabar kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye a halin yanzu.”
Ministan harkokin wajen Holland ya tabbatar da cewa ya yanke kauna kan cewa wannan matsayi na iya canjawa, yana mai cewa, “Wannan wani abu ne da ba zai canja ba nan da watanni ko shekaru masu zuwa, a kan haka hakurina ya kare, zan koma gida in rubuta takardar murabus dina,” a cewar shafin yanar gizo na Dutch News.
A nasa bangaren, dan majalisa Eric van der Burg na jam’iyyar People’s Party for Freedom and Democracy (VVD) ya ce “ya kadu da shawarar yin murabus.” Jam’iyyun adawa sun bayyana rashin jin dadinsu, inda suka yi imanin cewa Voldkamp ya gaza samun goyon bayan da ya dace kan wannan manufa tasa.
Veldkamp ya shaidawa kafafen yada labarai a ranar Alhamis cewa yana da niyyar daukar karin matakai kan Isra’ila. Sai dai muhawarar da ‘yan majalisar suka yi na tsawon sa’o’i biyar, ya nuna cewa akwai rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin , inda jam’iyyun BBB da VVD suka ki amincewa da matakin da ake Shirin dauka na kara matsa lamba kan Isra’ila