Miliyoyin musulmi a nan kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya suka gudanar da sallar Layyah, wanda yake daga cikin manya-manya bukukuwa a cikin addinin musulunci.
Tashar talabijin na Press tv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan sallar wanda maniyya da kuma sauran musulni suke yi ya hada da yanka dabba gwagwadon hali, da kuma raba namansa a tsakanin mabukata musulmi. Don tunawa da annabi Ibrahim a lokacinda ya yi kokarin yanka dansa annabi Isma’ila duk da cewa shi kadai ne yake da shi. Kuma yana sonsa, da yayi haka sai All..T ya fance shi da rago, don haka a mai makon dansa ya yanka rago,
Ana son duk musulmi baligi wanda ya ke da lafiya da ikon zuwa Hajja to yayi shi akalla sau
Guda a rayuwarsa.
A Bana dai musulmi kimani 1600,000 suka sauke farali. Mafi yawa daga kasashen waje.