Rasha ta ce hare-haren Ukraine a kan yankunanta, musamman na baya-bayan nan zasu fuskanci martani mai zafi.
Da yake sanar da hakan Mataimakin shugaban kwamitin sulhu na Tarayyar Rasha Dmitry Medvedev ya ce, sojojin kasar za su ci gaba da kai farmakin har sai an kawar da makiya gaba daya.
Ya kuma kara da cewa babu makawa Rasha za ta mayar da martani kan ayyukan zagon kasa da sojojin Ukraine suka yi.
A cewarsa, za a ci gaba da kai hare-hare ba tare da kakkautawa ba, kuma wadanda ke da alhakin wadannan ayyuka.
Hukumar tsaro ta Ukraine dai ta ce an kai wa wata gada mai muhimmanci hari da ta hada Rasha da yankin Crimea da bamabamai.
Ta ce an jera bamabaman ne masu nauyin kilogiram 1,100 a cikin ruwa na tsawon watanni kuma aka tashe su daga nesa jiya Talata.
Gadar da ake kiran ta Kerch, Rasha ce ta gina ta bayan ta mamaye yankin na Crimea a 2014 daga hannun Ukraine.
Karo na biyu kenan ana kai wa gadar hari tun bayan barkewar yaki tsakaninsu a 2022.