Hukumar dake kula da ‘yan hijira ta MDD ta yi gargadi akan cewa; an sami rubanyar kudaden aike wa da kayan agaji zuwa Sudan saboda yaki da Iran.
Hukumar ta ci gaba da cewa karuwar kudaden da aka samu na aikewa da kayan agajin ya haddasa tsaiko da kuma jinkirin isarsu ga mabukata.
Daga cikin matsalolin da ake fuskanta da akwai cunkuson jiragen ruwa a tasoshin jiragen ruwa, da karuwar kudin makamashi da na inshora.
Mai Magana da yawun hukumar ta ‘yan hijira ta MDD Carlotta Wolf, ta fada a birnin Geneva cewa; A halin yanzu ana sauya jiragen da suke daukar kayan agajin daga Dubai suke bi ta mashigar ruwan Hurmuz, da wasu daga nahiyar turai suke bi ta mashigar ruwan “Cape Of Good Hope” na kasar Afirka Ta Kudu.
Haka nan kuma ta ce, wannan sauyin hanyar zirga-zirgar da aka yi, ya sa kayan agajin na yin jinkirin kwanaki 25 kafin su isa.
Kudin da ake kashewa kuwa sun karu daga Dala 927,000 zuwa Dala miliyan 1.87.