Jami’an kare hakkin dan’adam na MDD sun nuna jin dadinsu dangane da hukuncin da kotun duniya ta manyan laifuka ( ICC) ta yanke akan mutum na farko da aka tuhumka akan laifukan Darfur na kasar Sudan.
A jiya Litinin ne dai kotun manyan laifuka ta duniya ta yanke hukunci akan Ali Muhammad ali Abd-Al-Rahman wanda ake yi wa lakabi da Ali Khushayb, bisa samunsa da laifi akan laifukan yaki a Darfur shekaru 20 da su ka gabata. Daga cikin laifukan da aka tabbatar da akan Ali Kushayb da akwai bayar da umarnin yi wa mutane da dama kisa, da kashe fursunoni biyu da gatari.
Alkalai uku ne su ka yi zaman shari’ar da aka yanke hukuncin tare da samun wanda ake zargi da laifin bayar da umarnin yin fyade a loakcin da gwamnatin Umar Hassan Al-Bashir take kokarin murkushe tawayen mutanen Darfur.
Mai Magana da yawun hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD, Seif Magango ya ce; Yanke hukuncin da kotun duniyar ta manyan laifuka ta yi, yana tabbatar da yarda da matsanaciyar wahalar da aka jefa mutanen Darfur da laifukan da aka tafka a kansu.
Shi dai Abd-Al-Rahman ya kasance jagoran rundunar ‘yan ina da kisa ta Janjaweed daga 2003-2004 da ta rika yi wa mutanen Darfur kisan kiyashi, da kona kauyukansu da dabbobinsu.