Kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric, ya soki HKI kan yadda take fadada mamayar da takewa yankunan kasar Siriya. Dujarric ya bayyana haka ne jim kadan bayan da firay ministan HKI Benyamin Natanyahu ya umurci sojojinsa su shiga yankuna kasar Siriya wadanda suke makobtaka da kasar tuddan Golan.
A ranar litinin da ta gabata ce Benyamin Natanyahu ya je har zuwa tuddan Golan inda ya bada wannan umurnin, sannan a gabansa sojojinsa suka fara mayar yankin Qunaitara na kasar ta Siriya.
Dujaric ya kara da cewa, yankunan da sojojin HKI suka mamaye ya sabawa yarjeniyoyin tsagaita wuta bayan yakin shekara ta 1967 da na shekara ta 1974.
Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa ya zuwa yanzu, sojojin HKI sun mamaye har zuwa kilomita 25 daga kan tuddan zuwa cikin kasar Siriya.