Babban magatakardar MDD Antonio Guterres wanda ya halarci taron da kasashen larabawa suke yi a Masar, ya bayyana goyon bayansa ga tsarin da su ka bijiro da shi na sake gina yankin Gaza, ba tare da an fitar da Falasdinawa daga cikinsa ba.
Gutress ya ce; Ina maraba da kuma nuna cikakken goyon bayana ga shirin da taron kungiyar kasashen larabawa ta bijiro da shi na sake gina Gaza.”
Gutrress ya kuma ce: MDD a shirye take ta shiga da karfi a yi wannan aikin da ita.
Haka nan kuma babban magatakardar MDD ya yi kira da a dauki duk matakin da ya kamata domin ganin ba a sake komawa yaki a Gaza ba.
Gutteres ya kuma ce, Gaza ba ta da makoma wacce ta wuce ta kasance a karkashin daular Falasdinawa.
Babban magatakardar MDD ya bayyana taron na kasashen larabawa da cewa yana da matukar muhimmanci domin daukar nauyi a jumlace da zai kai ga kawo karshen yakin Gaza.
A jiya Talata ne dai kasashen larabawa su ka hadu a Alkahira ta kasar Masar domin halartar taron tattauna hanyoyin sake gina Gaza da kuma kalubalantar manufar Amurka da HKI na korar Falasdinawa daga Gaza.