MDD Ta Ce Masu Fama Da Cutar HIV/AIDS Miliyon 6 Ne Zasu Mutu Saboda Janyewar Amurka Daga Tallafawa Hukumar UNAIDS

Hukuma mai kula da samar da magungunan HIV/AIDS ko (UNAISD) ta MDD ta bada sanarwan cewa mai yuwa mutane kimani miliyon 6 ne zasu mutu

Hukuma mai kula da samar da magungunan HIV/AIDS ko (UNAISD) ta MDD ta bada sanarwan cewa mai yuwa mutane kimani miliyon 6 ne zasu mutu a duk fadin duniya a cikin shekaru 4 masu zuwa saboda rashin samun tallafin Amurka a cikin shirin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayyana cewa, a ranarsa ta farko na kama aiki a matsayin shugaban kasan Amurka, ya dakatar da dukkan tallafin da Amurka take bayarwa a duniya na tsawon kwanaki 90.

Labarin ya nakalto shugaban shirin samar da magunguna HIV/AIDS Christine Stegling tana cewa, duk tare da cewa Amurka ta ci gaba da tallafawa HIV/AIDS na wucin gadi, amma suna ganin cewa da wuya hakan ya ci gaba don tun yanzu wasu al-amura sun fara tsayawa. Mai yuwa kome zai lalace nan gaba.

Stegling ta ce idan gwamnatin Amurka bata ci gaba da bada tallafi ga bangaren PEPFAR tsakanin shekara 2025-29 ba to kuwa yawan mace-mace saboda cutar Aids da HIV zai karu da kashi 400%. Wanda ya nuna cewa mutane kimani miliyon 6.3 ne zasu mutu a cikin wannan lokaci. Banda haka duk wani dakatarwa na tallafin sai ya shafi shirin gaba daya a duniya.

Ta ce a kwai mutane kimani 5000 suna aiki wa hukumar UNAIDS a kasar Habasha kadai, dakatar da tallafin yana nufin sun rasa ayyukansu. Sannan hukumar da aiki a kasashe 80 a duniya tare da tallafin daga kasashen duniya amma rabon Amurka ya fi yawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments