MDD Ta Bukaci Isra’ila Da ta Kawo Karshen Mamayar Da Tayi wa Yankunan Falasdinawa

Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma

Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma yace babu ja da baya game da kudurin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai

Sakataren ya sake yin kira ne saboda ya nuna irin bukatar da ake da ita wajen kare hakkin falasdinawa da kuma matsa kaimi wajen warware rikicin ta hanyar siyasa, adaidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza da labanon da kuma kasar siriya,

Wannan bayanin yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman dar-dar da cin zarafin dan adam ke kara Kamari a yankin Gaza da kuma gabar yammacin kogin Jodan, inda hankalin duniya ya tashi sosai na kashe fararen hula da ake yi , da tilastawa dubbai tserewa , sun bukaci kara kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Alummar falasdinu sun da hakkin a  kare musu hakkokinsu da yancinsu da kuma yi musu adalaci , da kuma hakkin tantance makomarsu  da kansu,  sai dai fiye da shekaru 2 ke nan an take musu hakokinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments