Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa kasashen duniya sun hadu a kan bukatar dakatar da wuta a Gaza, wanda sojojin HKI suka fara kaiwa hare hare tun watan Octoban da ya gabata.
Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto Guterres yana fadar haka a yau Litinin a ziyarar da yake yi a birnin Amman na kasar Jordan. Ya kuma kara da cewa yakamata a sanar da HKI kan cewa idan ta kai farmaki kan Rafah zata haddasa mutuwar Falasdinawa masu yawa a yankin.
Natanyahu Firai ministan HKI ya sha alwashin zai ci gaba da shirinsa na tura sojojinsa zuwa Rafah duk tare da gargani da kawaye da makiya suke masa kan hakan.
Guterres ya kammala da cewa kasashen Amurka da Turai da sauran kasashen musulmi sun hadu a kan cewa dole ne Natanyahu da fasa shirin na kai hare hare a Rafah saboda kaucewa mutuwar Falasdinawa da dama.