Hanyoyin yakin Isra’ila a Gaza sun yi daidai da kisan ƙare dangi, ciki har da fararen hula wadanda aka kashe tare da azabtar da Falasdinawa da gangan, a cewar wani Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na Musamman.
Harin bama-bamai da Isra’ila ta kai a unguwar Sheikh Radwan da ke birnin Gaza inda fararen hula ke zaune, ya kashe Falasdinawa akalla uku.
A wani hari na daban da aka kai a wajen makarantar Hamama, Isra’ila ta raunata Falasdinawa 10, in ji cibiyar yada labarai ta Falasdinu (PIC).
Har ila yau Isra’ila ta tsananta kai hare-hare a duk fadin Gaza, inda aka harba makaman atilari a yankunan kudanci da gabashin unguwar Zeitoun.