Mataimakin Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Hari Kan Iran Gwajin Karfinta Ne A Fagen Kimiyya Da Fasaha

Mataimakin shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Yakin kwanaki 12 da aka kaddamar kan Iran, gwaji ne na karfinta a fagen kimiyya da fasaha Mataimakin

Mataimakin shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Yakin kwanaki 12 da aka kaddamar kan Iran, gwaji ne na karfinta a fagen kimiyya da fasaha

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Arif ya bayyana cewa: Wani bangare na ci gaban Iran a fannin kimiyya da fasaha na da nasaba da mayar da takunkuman da aka kakaba mata zuwa ga damammaki da bunkasa ci gabanta.

Ya yi bayanin cewa: “Yakin kwanaki 12 da gwamnatin Sahayoniyya da Amurka suka kakaba wa Iran, wani gwaji ne kan karfin kimiyya da fasaharta. Ya ce: Iran ta fi karfi tare da mai da hankali a bangarorin kimiyya da fasaha.”

Arif ya jaddada cewa: Al’ummar Iran suna bin tafarkin shahidai da kuma ci gaba da bin tafarkin martaba da ci gaban kasarsu, a tsawon shekaru takwas na yakin kare kai da Iraki ta kakaba wa Iran, da kuma tsawon kwanaki 12, jami’o’i sun gabatar da shahidai salihai domin kare gwamnatin kasar da ma al’ummar Iran masu girma, don haka suna rokon Allah da ya baiwa iyalan wadannan shahidai masu daraja hakuri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted