Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran.

A wani bangare na huldar duplomasiya tsakanin iran da saudiya , mataimakin ministan harkokin wajen kasar saudiya Saud bin mohammad Al-sati ya gana da ministan

A wani bangare na huldar duplomasiya tsakanin iran da saudiya , mataimakin ministan harkokin wajen kasar saudiya Saud bin mohammad Al-sati ya gana da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a nan birnin tehran inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafin alakokin dake tsakani da kuma ci gaban yankin.

Ganawar wani bangare ne na kokarin da kasashen biyu ke yi na kara karfafa dangantakar dake tsakaninsu da kuma ci gaba da tattaunawa kan batutuwa masu tsauri, saudiya da iran sun kara fifita huldar diplomasiya domin shawo kan rikicin da ake ciki a yankin da kuma samar da damarmakin yin aiki tare.

Ganawar tasu ta zo ne adaidai lokacin da ake cikin mawuyacin halin a yankin  da suka hada da yankin falasdinu, labanon da kuma kasar siriya, dukkan kasashen suna taka muhimmiyar rawa a lamurran da suka shafi yankin, tattaunawa ta kai tsaye itace mafita na rage matsalolin da kuma bayyana damuwarsu.

Ana sa bangaren Saud bin mohammad Sati mataimakin ministan harkokin wajen saudiya ya jaddada muhimman kara karfafa alaka da kuma yin aiki tare domin fuskantar kalubalen tsaro da yankin ke ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments