Daruruwan masu Zanga-zanga a Taiwan sun bukaci ganin an kawo karshen yakin da ake yi a Gaza, tare da yin kira da gwamnatin kasar tasu da ta yanke sayar wa da kamfanonin HKI da kuma Amurka.
A jiya da dare ne dai aka daruruwan mazaunan babban birnin Taiwan, Tape, su ka yi jerin gwano daga ne nuna goyon bayansu ga Falasdinawa.
Masu jerin gwanon sun daga tutocin Falasdinu da kwalaye da aka yi rubutu akansu na yin tir da hare-haren da HKI take kai wa a Gaza.
A cikin kasashe da dama na duniya ana yin jerin gwano da kuma Zanga-zangar yin kira da a kawo karshen yakin Gaza da kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa.