Dubban daruruwan masu zanga-zanga a biranen Barlin Paris da kuma Stockholm ne suka bukaci gwamnatocin kasashensu su kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a gaza, su kuma tabbatar da cewa abinci ya isa gaban Falasdinawa a Gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga-zangar sun kira ga gwamnatocin kasashensu su dakatar da bawa HKI makaman da take kishe falasdinawa da su.
A birnin Berlin da kasar Jamus dubban Jamusawa sun hadu a dandalin at Oranienplatz inda suke rera taken ‘a bawa Falasdinawa yenci, HKI yar ta’adda ce, kuma gwamnatin Jamas ta dakatar da tallafin da take bawa HKI. Labaran sun kara da cewa hatta mutanen kasar Jamus yan asalin yahudawa sun fito sun bayyana cewa ba da sunansu ne HKI.
A birnin Paris na kasar Faransa masu zanga zangar suna fadar cewa ba wanda yake da hakkin mamayar wata al-umma ya kuma ce sai sun kaura sun bar mashi kasarsu.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar suna fadar shi’arin cewa HKI mai aikata laifin yaki ne kuma Macron yana da hannu a cikin laifin nata.