Masu Zanga Zanga A HKI Sun Bukaci Natanyahu Da Gwamnatinsa Su Yi Murabus

Yahudawan Sahyoniyya, a darare uku a jere suna fitowa kan tituna a biranen HKI tare da bukatar Benyamin Natanyahu firai ministan kasar da kuma majalisar

Yahudawan Sahyoniyya, a darare uku a jere suna fitowa kan tituna a biranen HKI tare da bukatar Benyamin Natanyahu firai ministan kasar da kuma majalisar ministocinsa masu tsatsauran ra’atin addini su sauka daga mukamansu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan na cewa dubban daruruwan mutane ne suka fito kan titunan Rehovot, Hod Hasharon da kuma Tel Aviv kwanaku uku a jere, suna bukatar gwamnatin kasar ta amince da yarjeniyar tsagaita wuta a gaza don dawo da fursinonin yakin yahudawan wadanda suke hannun kungiyar Hamas, su dawo da ransu.

Kafin haka dai dakarun Hamas sun kashe yahudawa 6 suka kuma jefa  gawakinsu a wani wuri a gaza, inda sojojin yahudawan suka ganosu.

Kungiyar ta bayyana cewa idan Natanyahu da Amurka suna bukatar sauran fursinonin da ransu to su dakatar da yaki a gaza .

A halin yanzu dai natanyahu ya dage kan cewa sojojin HKI ba zasu bar gaza ba ko da an kuwa karshen yakin saboda kada a shigo da makamai gaza bayan an tsagaita wuta.

Natanyahudawa ya dauki watanni kimani 11 yaya fafatawa da hamas saboda kwatoyahudawan da suke hannunsu amma ya kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments